Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya mayar da tsohon shugaban hukumar Hisbah Sheikh Aminu Daurawa kan mukaminsa na shugabancin hukumar.
Shehin malamin ya tabbatar da cewar tuni ya karbi takardar kama aiki a ofishin sakataren gwamnatin jihar Baffa Bichi.
Daurawa wanda ya ce ya karbi aikin ne saboda ya ga gwamnati mai ci ta Abba Gida-gida da gaske take, inda ya ce zai mayar da hankali wajen aurar da zawarawa kamar yadda gwamnati take shirye-shiryen aiwatar wa