Iran ta sha alwashin murkushe masu da’awar a daina sanya hijabi
“Hukuncin masu ingiza mata su dinga cire hijabansu ya fi na cirewar tsauri” in ji wani jami’in Iran da yake tattauna wa da Jaridar Meh news
Mataimakin Ministan Shari’a na Iran Ali Jamadi ya sanar da cewa mutanen da ke kira ga mata da su dinga cire hijabansu za su gurfana a gaban kuliya kuma a tuhume su da aikata mummunan laifin da babu zabin daukaka kara.
Kalaman na Jamadi a karshen makon da ya gabata na zuwa ne a lokaci da wasu mata a Iran suke bijirewa ka’idar sanya sutura, suna yawo ba hijabi a manyan kantina, gidajen sayar da abinci da shaguna da tituna da sauran wuraren taruwar jama’a.
Mata shahararru da dama a ‘yan watannin nan a Iran sun dinga fitar da hotunansu babu dan kwali ko lullubi a shafukan sada zumunta na yanar gizo.
Kafar yada labarai ta Mehr News ta rawaito Jamadi na cewa “Hukuncin masu ingiza mata su dinga cire hijabansu ya fi na cirewar tsauri, saboda hanya ce karara ta ingiza mutane su lalace.”
Sai dai Ministan Bai ambaci irin hukuncin da za a yi wa wanda ya aikata wannan laifi ba