Binani ta garzaya gaban babbar kotun tarayya da ta karbar mata nasarar ta da tayi

Yar takarar gwamna ta jam’iyar APC a jihar Adamawa sanata Aishatu Binani ta shigar da karar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da abokin takarar ta na jam’iyar PDP Umar Fintiri a gaban babbar kotun tarayya dake zamanta a birnin tarayya Abuja

Binani na karar hukumar zaben ne akan soke nasarar da tayi wanda INEC ta ambata tun da fari.

A cewar Binani ba hurumin hukumar zabe ne ba bayan ta ayyana wanda yayi nasara kuma ta dawo ta soke nasarar tata daga baya

Tace wannan hurumi ne na kotu a don haka take rokon kotu ta sake duba aikin da hukumar zaben ta gudanar na ranar 15 ga watan Afrilu.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments