Gwamna Ganduje ya damka alhakin rufe guraren hada-hadar kudade da suka daina karbar tsoffin kudade

Gwamnatin Kano ta ce zata rufe duk gurin da ya ƙi karɓar tsohon kuɗi a hannun jama’a

Shugaban Hukumar kula da Zirga-zirga Ababen Hawa ta jiha KAROTA Hon. Baffa Babba Dan’agundi ya bayyana hakan a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na Hukumar, Nabilusi Abubakar
K/Naisa ya rabawa manema labarai a yau Litinin 13/02/2023

Ya ce tuni Mai Girma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da umurnin rufe duk wani gurin kasuwanci a faɗin jihar nan wanda yaƙi karbar tsofaffin kuɗi

Baffa Babba ya ce an ɗauki matakin ne saboda ƙorafe-korafen jama’a da ya yi yawa na ƙin karɓar tsofaffin kuɗin a hannun jama’a musamman a wasu daga cikin gidajen mai da Asibitoci da wajen saye da sayarwa na faɗin jihar nan

Hakan ya biyo bayan umarnin da babban bankin ƙasa CBN ya bayar na ci gaba da karbar tsofaffin kuɗin.

Tuni dai Mai Girma Gwamna ya bayar da umurni ga Kwamitin Kar-ta-kwana mai kula da gidaje Mai su fita su tabbatar ana karɓar tsofaffin kuɗin

Ya bayyana cewa duk wanda yaƙi bin umarnin ya saɓa da dokar Hukumar kula da Haƙƙin mai saye da sayarwa ta Consumer Protection Council, sashe na 10 ƙaramin sashi na 1(b) da kuma sashe na 10 ƙaramin sashi na 2 na dokar Hukumar

Ya ƙara da cewa duk wanda aka kama za a rufe wajen kasuwancinsa tare da gurfanar da shi a gaban Shari’a domin daukar mataki na gaba

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments