Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta wallafa cewa tayi watsi da sakamakon wasu rumfunan zabe da aka samu hatsaniya yayin gudanar da zabe a guraren a jihar Kogi.
Kwamishinan hukumar dake tattara sakamakon zaben jihar Kogin Dacta Hale Longport, shine ya sanar da hakan inda yace lamarin soke zaben zai hada da wasu kananan hukumomi
A zantawar sa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN yace sun Sami rahoton ayyukan Daba yayin gudanar da zaben wasu gurare da suka hada da Anyigba da Dekina a karamar Hukumar Kogi ta Gabas da mazabar Mopa a Kogi ta yamma da kuma wasu bangarorin karamar hukumar Kogi ta tsakiya.