Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta sanar da cewa ta kama wata mata dauke da katinan zabe guda 20 a jihar Benin
Matar mai suna Comfort Muoneke, an kame tare da mata biyu da ke tare da ita
A jawabin da ta wallafa a shafin ta na Facebook hukumar ta EFCC tace jami’an ta masu kula da shiyyar Benin sune suka sami nasarar cafke wadannan mata uku