Tsohon mataimakin shugaban kasa Alh Atiku Abubakar ya mika sakon ta’aziya ga Iyalan Oladipo Diya na rashin da suka yi na babban jami’in soja
An Sami labarin rashin ne a sanarwa da ɗansa Barrister Oyesinmilola Diya, ya fitar a madadin sauran iyalansa, ya tabbatar da mutuwar tsohon babban jami’in sojin da safiyar ranar Lahadi.
An dai haifi Janar Oladipo Diya a garin Odogbolu na jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya, yana daga cikin dakarun da suka yi yaƙin basasar ƙaasr nan kafin ya zama babban hafsan sojin ƙasar nan a shekarar ta 1993.
Ya kuma riƙe muƙamin mataimakin shugaban majalisar mulkin soji na ƙasa a shakerar 1994.
Atiku yace tarihi bazai manta da wannan Dan tahaliki ba.