Gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele ya gana da ministan kwadago, criss Ngige, a yammacin yau Litinin 27-03-2023.
Ganin ya biyo bayan shirin kungiyar yan kwadago na shiga yajin aiki a ranar Laraba mai zuwa.
Emefiele ya roki Ministan da yasa baki wajen dakatar da yajin aikin da kungiyar ta dauki gabarar farawa a ranar Laraba.
Taron ya sami halartar manya daga kungiyar yan kwadago da kuma shuwagabanni daga babban bankin Najeriya CBN
Emefiele yace tuni ya wadata bankunan yan kasuwa da takardun kuɗi.