Shugaban yakin Neman zaben Dantakarar Gwamnan jihar kano a zaben shekara ta 2023 a jamiyyar APC Dr. Umar Tanko yakasai, ya shawarci alummar jihar kano da kasa baki daya, da su kasance masu zabar nagartattun mutane da za su kula da hakkokinsu da sauke nauyi da alkawarin da suka dauka a lokutan yakin Neman zabe.
Dr. Umar Tanko ya bayyana haka ne,a lokacin da yake zantawa da manema labarai dangane da gwanayensa Dr.Nasuru Yusuf Gawuna da Dantakarar shugabancin kasa Asiwaju Bola Ahmed Tunubu,bisa gudunmawar da suka bayar a lokutan baya da suka gabata,Wanda ya gudana a gidansa dake nan jihar kano.
Yace,Alummar jihar kano, mutane ne, da suke da ilimi da basira da ajiye abubuwan tarihi akan duk wasu shugabanni da suka jagarancesu ,inda yace,alumma sun San Waye Dr.Nasuru Yusuf Gawuna da rawar daya taka tun daga shugabancin karamar hukumar Nassarawa da kwamishinan Gona har zuwa mataimakin Gwamnan kano,to koda wannan yakamata alumma su bibiya tare da dorashi a mizani domin zabarsa a matsayin Gwamnan jihar kano a 2023 mai zuwa.
Yace, Dr.Nasuru Yusuf Gawuna, ya tallafawa alumma ta fannoni da dama da suka hadar da baiwa dalibai tallafin karatu da Samar da magudanan ruwa da bunkasa kasuwanci musamman, bangaren harkokin Noma da taimakawa matasa da kungiyoyi da dama.
Dr.umar Tanko yakasai,ya kara da cewa, ta bangaren kyakyawar muamulla da jama,a bashi da fishin kowa ko gaba da wasu ko cin mutuncin abokanan burmin siyasa saboda basa tutar jamiyya guda,inda yace yana girmama manya da malamai da sauran alummar jihar kano da kasa baki daya.
Ya sha alwashin cewa,idon Dr.Nasuru Yusuf Gawuna, ya zama Gwamnan kano a zaben shekara ta 2023,tabbas zai cikawa alummar jihar kano alkawarirrikan da jamiyyar APC tun daga kasa har jiha suka daukar musu,da hadar da :Samar da tsaro da bunkasa tattalin arzikin kasa.
Samar da tsaro yana daga cikin jigon ci gaban kowacce kasa,saboda idon babu tsaro babu kwanciyar hankalin jama,a,Sai kuma,farfado da tattalin arziki Wanda ya shafi fannoni da dama na rayuwar alumma.
Dr.Umar yakasai, yace akan haka,Dantakarar shugabancin kasar nan a jamiyyar APC Bola Ahmed Tunubu,ya Samar da littafi mai dauke da manufofin da jamiyyar APC za ta fara kallo da zararar sun samu darewa kan shugabancin kasar nan a shekara ta 2023.
Daga cikin abubuwan da suka fitar akwai,farfado da kamfanonin da suka durkushe da Samar da wutar lantarki da bunkasa kasuwancinsu da noma da Samar da gidaje ga alummar kasa domin su samu saukin mallakar nasu da tallafawa fannin harkokin ilimi da Samar da sana,oin dogaro da kai ga matasan yankunan kudu da arewacin kasar nan ta hanyar amfani da ilimin kimiyya da fasahar sadarwar zamani,domin yakar talauci a jihohin kasar nan baki daya.
Shugaban yakin Neman zaben Gwamnan jihar kano, Dr. Umar, yace wannan ba zai samu ba,Sai alummar jihar kano sun ba da hadin kan daya dace wajen samarwa yantakarkarun jamiyyar APC tun daga jihohi har kasa baki daya.
Ya kuma shawarci alummar jihar kano da su kasance masu kulawa da sanya yantakarkaru a mizani domin Samar da shugabanni na gari da za su bunkasa kasa da alummarta ta bangarori da dama, yadda kasar nan za ta yi gogayya da sauran kasashen Duniya.
Ya kara da cewa, jamiyyar APC ta shirya tsaf wajen samarwa yankasa sauye sauyen da suka kamata, kasancewar alumma suna bukatar tallafin gaggawa da za su inganta rayuwarsu da alfahari da Wanda suka jajirce wajen zabarsu,inda yace,ba za su baiwa maras ‘Da’ kunya ba.
Daga karshe yace wannan shugabancin da za,a gudanar a jamiyyar APC, shugabanci ne da za,a yi shi tare da alummar jihar kano musamman matasa maza da mata domin baiwa kowa damar sharbar roman damakaradiyya yadda ya kamata, ba tare da kaucewa alumma sanin abubuwan da suke gudana ba a shugaban ce.
Wakilin AKSAM MEDIA ,Ibrahim sani gama, ya rawaito mana cewa,umar Tanko yakasai, yana da tabbacin Dantakarar shugabancin Gwamnan jihar kano a jamiyyar APC, Dr. Nasuru Yusuf Gawuna ba zai bawa maras ‘Da kunya ba in har ya zama Gwamnan kano a shekarar 2023 mai zuwa.
Ibrahim sani gama kadaura24.