Dan takarar Shugaban kasa na jam’iyar NNPP, Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya ce ba wanda zai yi asarar kudin sa matukar ya hau karagar mulki.
Kwankwaso wanda ya bukaci gwamnati ta sauya matsaya kan batun canjin, ya ce rashin yin hakan zai jefa Najeriya cikin babban kalubale.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke korafin tuni wasu sun daina karbar kudin gabanin wa’adin karshen watan nan.
Rabi’u Kwankwaso ya ce yana takaicin yadda babban bankin ya ki amincewa da hatta kiran majalisar dokoki na kara wa’adin canjin.
Rahotanni na nuna a sassan Najeriya wasu kasuwanni sun dakatar da hada-hadar kasuwanci gaba daya
Yanzu dai za a jira a ga ko babban bankin zai saurari barazanar Majalisa ta sa kafar wando daya da Emefiele.