Rundunar yan sanda ta cafke yan ta’adda 208 a wata jiha

Rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen  jihar Adamawa tayi nasarar kama mutane 208 da ake zargi da aikata manyan laifuffuka daban daban.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar,  Sikiru Akande ya tabbatar da kama wadanda ake zargi da aika laifuffuka daban daban yayin wani taron manema labarai da ya gudana a shedkwatar rundunar ‘yan sandan jihar.

Akande ya ce sun kama mutane 208 da laifin  aikata laifuffuka da suka hada da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, fashin daji da sauran miyagun laifuka, kuma daga cikinsu tuni sun aike da 108 zuwa gaban kuliya domin fuskantar shari’a, sannan sun gabatar da 100 da ke hannunsu a gaban manema labarai.

Ya kuma kara da cewa sun yi nasarar kwato bindigogi kirar AK-47 guda 7 da kuma wasu bindigogi kirar hannu da dama a ciki da wajen jihar.

Taron Manema Labarai Na Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa
Taron Manema Labarai Na Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa

A hirar shi da Muryar Amurka, Yakubu Ibrahim, daya daga cikin wadanda aka kama da zargin laifin garkuwa da mutane ya ce ya kirawo wani mutum da nufin zai yi garkuwa da shi in dai bai bashi wasu makudan kudade ba, kafin daga bisa ni kuma ‘yan sanda suka kama shi.

Shi kuwa Yusuf Muhammad mai shekaru 18 da haihuwa, yana daya daga cikin wadanda aka kama da manyan bindigogi kirar AK-47 guda hudu, wanda ya ce abokanansa ne daga Kamaru suka zo suka bashi ajiyar wadanda nan bindigogin.

Harsasai Da 'Yan sanda Suka Kama a Adamawa
Harsasai Da ‘Yan sanda Suka Kama a Adamawa

A nasa bayani, wani mai suna Muhammad Musa, wanda rundunar ta kama yana yi wa ‘yan sandan jihar sojan gona ya bayyana cewa, yana daya daga cikin ‘yan kungiyar sa kai a jihar, inda daga bisani abun ya rike ya koma amfani da kayan ‘yan sandan jihar yana saka shinge yana kwacewa mutane kudi.

Ko a watan Disamban bara, rundunar ‘yan sanda jihar Adamawa ta yi nasarar kama mutane 108 da ake zargi da garkuwa da mutane da wasu sauran manyan laifuffuka

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments