Yadda Sinawa ke gudanar da murnar kawar da cutar Korona zuwa matakin B

A jiya Alhamis aka cika  kwana na 11 da kasar China ta mayar da cutar COVID-19 zuwa rukunin B a kasar.

Bisa bayanin da hukumar kiwon lafiya ta kasar ta yi, an ce, yawan mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 mai tsanani ya fara raguwa a larduna daban daban na kasar.

Kawo Yanzu Sinawa suna maraba da zuwan bikin Baraza cikin koshin lafiya. An kuma samu wannan yanayi ne domin Sin ta dauki matakan yaki da cutar COVID-19 yadda ya kamata, wadanda suka samar da manyan nasarori a kasar.

A cikin shekaru 3 da suka gabata, gwamnatin kasar Sin ta yi kokarin tabbatar da lafiyar dukkan jama’arta. Sin ta yi ta gabatar da kididdiga da bayanai game da cutar ga kasa da kasa, don samar da gudummawa wajen yaki da cutar, da nazarin alluran rigakafin cutar, da kuma kayayyakin gwajinta.

Game da tattalin arziki kuwa, Sin ta raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma yayin da take tinkarar cutar ta COVID-19, wadda ta kasance kasa dake kan gaba wajen farfardo da tattalin arzikin duniya.

Yanzu haka China  ta kara bude kofa ga kasashen waje, hakan ya tabbatar da samar da kayayyaki a duniya yadda ya kamata.

Kazalika ta sanar da cewa har yanzu ba a ga bayan cutar COVID-19 a duniya ba,  ya kamata kasa da kasa su yi kokari tare don tinkarar kalubalen.

China tace za ta kara  kaimi ga hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa wajen yaki da cutar Covid-19 da kuma samar da gudummawa wajen farfado da tattalin arzikin duniya baki daya.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments