Mutane 24 sun rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da iska da ta shafi mutane kimanin 2000 a jihar Katsina.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, bada agajin gaggawa ta NEMA Umar Muhammad ne ya bayyana hakan a zantawar sa da Kamfanin Dillancin Labarai na kasa NAN.
Muhammad ya ce an samu rahoton afkuwar ambaliyar a dukkanin kananan hukumomin jihar 34 a lokacin damina kuma abin ya shafi mutane 18,245.
Ya ce wasu mutane da dama sun samu raunuka daban-daban a sakamakon bala’o’in. Kakakin hukumar ya kuma ce gidaje 16,625 ne suka lalata sakamakon ambaliyar.
A cewarsa, gonaki 1,620 kuma sun nutse a cikin kananan hukumomin Kafur, Danja da Ingawa inda aka yi asarar dukiyoyi da amfanin gona da aka yi kiyasin sun kai miliyoyin naira sakamakon iftila’in.
Mohammed ya kara da cewa nan ba da jimawa ba jihar za ta fara rabon tallafi ga wadanda abin ya shafa.
Kakakin NEMA, yace hukumar su nan ba da jimawa ba za ta raba kayan agaji ga wadanda abin ya shafa.