A kokarin na tsaftace jihar Kano daga ayyukan Daba da sace-sace Hukumar tsaro ta NSCDC ta kasa reshen jihar Kano ta samu nasarar kama wadansu mutane biyar da ake zargi su da aikata Dabiar nan ta kwacen wayoyin al’umma
Bayan samun nasarar cafke wadannan matasa biyar Hukumar a yanzu haka tana neman Karin wadansu mutane biyu da ake zargin suna siyan wayoyin sata daga hannun barayin wayar.
Sanarwa da hukumar NSCDC ta fitar ta bakin daraktan yada labarai na hukumar, Ibrahim Abdullahi ta ce wadanda ake zargin an kama su ne a ranar Talata 23 ga watan Mayu a Unguwar Sabon Gari da ke karamar hukumar Fagge.
“Wadanda ake zargin Faisal Usman mai shekaru 28 da Mansur Isa mai shekaru 38 sai kuma Abdullahi Bashir, 25 da Ahmed Ibrahim, 21 sai kuma Zulkifil Bello mai shekaru 25.
“Suna aikata muggan laifuka a yankin Sabon Gari a karamar hukumar Fagge da ke jihar inda suke kwace wayoyin mutane da basu ji ba kuma basu gani ba.
“Jami’an mu na bangaren tattaro bayanin sirri yanzu haka sun bazama neman sauran wandanda suka hada kai, Abdullahi da Sunday wadanda sune suke siyan wayoyin sata da kuma layukan waya.