Cibiyar bincike da maganin cutar daji NICRAT ta bayyana damuwarta a game da rahoton samun sinadarin ethylene oxide a cikin INDOMIE INSTANT Noodles na musamman mai dandanon kaza.
Hukumar NAFDAC ce ta yi gargadi bayan da binciken hukumomin Malaysia da Taiwan ya gano wannan lamarin.
Ko da yake, shugabar NAFDAC Farfesa Mojisola Adeyeye a ranar Talata, ta bayyana cewa, taliyar indomie da ake yi a gida Najeriya ba ta da illa.
A wata sanarwar da ta fitar a jiya Laraba, babban Darektan NICRAT Farfesa Usman Malami Aliyu, ya yabawa NAFDAC da daukar matakin kariya cikin gaggawa gami da kaddamar da binciken lamarin, kamar yadda jaridar vanguard ta wallafa.
Darektan ya ce, nan da ‘yan watanni zuwa ‘yan shekaru masu zuwa, za a samu karuwar bayyanar nau’ukan cutar daji dabam-dabam bisa ga tsawon lokacin da mutane suka dauka suna cin taliyar Indomin.
A shekara ta 2020 kawai, ‘yan Najeriya dubu saba’in da takwas ne suka mutu a sanadiyyar cutar daji, a cewar shugaban cibiyar binciken ta NICRAT, farfesa Aliyu.
Aliyu, ya shwarci jamma’a da su yi aiki da umurnin NAFDAC na haramta cin indomie Instant Noodles slecial mai dandanon kaza.
Sanarwar cibiyar ta kara da cewa “zamu cigaba da yin hadin gwiwa da NAFDAC domin tabbatar da kariya da lafiyar ‘yan Najeriya daga cin sinadarin dake haifar da cutar daji”.
Sinadarin Ethylene oxide wani sinadari ne mai tasiri da ake amfani dashi wajen sarrafa glycol ethers wani sinadari da ake amfani da shi wajen hada fenty da sinadaren tsaftacewa, polyglycol ethers -wani sinadarin da ake amfani da shi wajen hada sinadaren tsaftacewa, sabulu da kayan kwalliya, emulsifiers-wani sinadarin da yake taimakawa wajen hadewar abinci, detergents da solvents.
Kana, ana amfani da sinadarin dake daskarewa wajen tsaftace kayyayakin abinci da kayan yaji, kayayyakin aikin asibiti musamman ma wadanda tsaftacesu a wuta yake musu illa.