Bayan kaiwa Putin hari, tsohon shugaban Russia ya bukaci a kashe shugaban kasar Ukraine

Rasha ta zargi Ukraine da yunkurin kai hari da jirage marasa matuka a fadar Kremlin da nufin kashe shugaba Vladimir Putin, zargi mafi ban mamaki da Moscow ke yi wa Kyiv tun bayan yakin da ya barke a watan Fabrairun 2022.

Sai dai Ukraine ta dage cewa ba ta da alaka da harin da ake zarginta da kai wa, tana mai nuni da cewa Rasha ce ta shirya shi, yayin da Amurka ta ce ya kamata a dauki rahoton a matsayin kanzon kurege.

Ko da yake fadar Kremlin ta ce Putin bai ji rauni ba kuma ba a samu asarar rai ba.

A ranar da aka ce an kai harin, gwamnatin Kyiv ta ce harin da Rasha ta kai ya kashe mutane 21 a yankin Kherson da ke kudancin Ukraine, ciki har da wani babban kanti da tashar jirgin kasa.

Sanarwar da gwamnatin Kremlin ta fitar ta ci gaba da cewa, Rasha na da hakkin daukar matakin ramuwar gayya a duk inda taga dama kuma a lokacin da ta ga ya dace.

Shi ma sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya nuna shakku kan sahihancin rahoton.

An yi kiraye-kiraye a Moscow don mayar da martani mai tsanani akan Ukraine inda tsohohon shugaban kasar Dmitry Medvedev ya yi kira da a kawar da Zelensky daga doron kasa.

Labarin na Kremlin ya zo ne a daidai lokacin da Ukraine ke shirin kai wani sabon hari da nufin fatattakar sojojin Rasha daga yankin da suke rike da su a halin yanzu a gabashi da kudancin kasar.

Zelensky ya ce an kashe mutane 21 a yankin Kherson a hare-haren da Rasha ta kai kan birnin da sojojin Ukraine suka kwato a watan Nuwamban bara da kauyukan da ke kusa da su.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments