Hukumar tsaro ta jar kwala taci alwashin yaki da masu yin kudin Bogi
Hukumar dake kula tare bada tsaro ga kadarorin gwamnati ta jar-kwala taci alwashin kama tare da gurfanar da duk wanda ta samu yana ta’ammali da kudin jabu a gaban kotu.
Shugaban Hukumar na kasa Ahmed Audi shine ya bayyana hakan a zantawar sa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN
Yace hukumar sa ta jar-kwala ba zata yi kasa a guiwa ba wajen sintirin tare da kama duk wanda ta samu da taadar yin zagon kasa ga tattalin arzikin Najeriya
Ya kara da cewa kawo yanzu hukumar sa ta kama miliyoyin kudaden jabu a jihohi da dama na kasar nan.