Gwamnati ta saka dokar hana fita a jihar Kaduna
Biyo Bayan barkewar wani rikici da yayi sanadiyar mutuwar mutane 10 a karamar Hukumar Zagon Kataf yanzu haka gwamnatin Kaduna ta ayyana dokar ta baci a garuruwan Ungwan Juju, Mabuhu, Ungwan Wakili da Zangon Urban.
Rahoton da aka rabawa manema labarai daga shugaban karamar hukumar Zango Kataf, Yabo Ephraim, yace dokar ta zama wajibi ne bayan da aka sami gawarwakin mutane 10 a unguwar Wakili a cikin garin Zango Kataf
Ya kara da cewa tuni an Baza jamian soji dan dawo da zaman lafiya a yankunan.
Rahoton yace kawo yanzu yan sanda suna yin abin da ya dace