Kotun ƙwadogo a kasar Afirka ta Kudu ta bayar da umarnin dakatar da yajin-aikin da ma’aikatan jinya da malaman makaranta ke gudanarwa na neman ƙarin albashi a kasar.
Hukumomin lafiya na ƙasar sun yi na am da hukuncin, suna masu cewa hakan zai taimaka musu wajen aiwatar da tsarin hana albashi ga duk ma’aikacin da bai je wajen aikinsa ba, matuƙar yajin-aikin ya ci gaba.
Ana kallon ma’aikatan lafiya a ƙasar a matsayin masu aiki na musamman inda aka haramta musu shiga yajin aiki.
Dubban ma’aikatan ƙwadogon ƙasar na cikin yajin-aiki tun cikin makon da ya gabata kan rigimar ƙarin albashi.
An girke dakarun soji zuwa wasu asibitocin ƙasar bayan da aka samu rahotonnin da ke cewa ma’aikatan jinyar waɗanda ba su shiga yajin-aikin ba, na fuskantar tsangwama.
Ministan lafiyar ƙasar ya alaƙanta mutuwar majinyata huɗu da yajin-aikin, to sai ƙuniyar ma’aikatan ta ce mutuwar majinyatan ba ta da alaƙa da yajin-aikin nasu.