FARFESUN KABEJI
KAYAN HADI :-
1_KABEJI
2_ALBASA
3_NAMA
4_MAGGI, DA GISHIRI
5_MANGYADA
6_JAN TATTASAI
7_KOREN TATTASAI
Yadda za’ahada
Dafarko uwar gida zaki samu kabeji babba maikyau, saiki yanke wannan jijiyoyin masu kauri na jiki,sai ki yayyanka ki zuba aruwa kiwankeshi tas,kitsameshi a kwandon tace taliya ko salat,kibarshi yatsane,saiki dauko albasa kibareta kiyanta yanka maikyau akwance itama kiwanketa ki ajje daban, saiki dauko koren tattasai da jan tattasai kiyankasu kanana a ajje gefe,inkinga kinada wadata zaki iya saka karas da green Bean’s da peas,inbabu saikiyi da tattasan da albasar.
Sannan ki tafasa nama da albasa maggi gishiri,citta thyme inkinaso, inya tafasu saiki tsameshi daga ruwan kibarshi yadan tsane,saiki dauko kaskon suya kizuba mai inyayi zafi kiyanka albasa,saiki soya naman ammafa naman bada yawaba akesakawaba,kamar yanka goma ko sha biyu kanana,idan kuma ba halin saka nama saiki barshi,bayan kinsoya naman saiki tsameshi acikin man,saiki zuba yankakkun tattasai da albasar nan, kisoyasu ammafa basosai ba karsu kone,saiki dauko kabejin kizuba akai sai ki dauko maggi,kisa seasonings da dan kori,kizuba akai kijuya saiki dauko ruwan naman da kika tafasa kizuba aciki idan ruwan yayi kadan saiki kara ruwa,sannan kidauko naman dakikasoya kizuba aciki kijuya sosai yadda kayan hadin zasu hade jikinsu, saikirufe kirage wuta kibarshi zuwa yan mintuna