Hukumar FBI ta kusa gidan Joe Biden Dan gudanar da binciken sirri

An ba da rahoton cewa Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka (FBI) ba ta gano “takardun sirri” a binciken da aka yi a gidan Shugaban kasar Amurka, Joe Biden a jihar Delaware ba.

Lauyan Joe Biden, Bob Bauer ya bayyana a cikin wata rubutacciyar sanarwar da ya fitar cewa, an fara binciken ne tun daga karfe 08:30 ta safiya zuwa tsakar rana, kuma ba a samu wata “takardar sirri” a binciken da aka gudanar a gidan ba.

A gefe guda kuma, Bauer ya rawaito cewa sakamakon binciken, Ma’aikatar Shari’a ta tantance wasu rubuce-rubucen da Biden ya bari daga lokacinsa a matsayin mataimakin shugaban kasa.

Richard Sauber, daya daga cikin masu ba Joe Biden shawara ya bayyana a ranar 9 ga watan Janairu cewa an gano wasu “takardu dauke da bayanan sirri” daga wa’adinsa na mataimakin shugaban kasa a ofishin Biden na sirri da ke Cibiyar Penn Biden, a ranar 2 ga watan Nuwamban shekarar da ta gabata.

A ranar 22 ga watan Janairu, an bayyana cewa an samu sabbin “takardun sirri” a garejin gidan Shugaban kasar a Delaware.

Biden ya ce ya yi matukar mamaki da ya ji cewa an gano wasu takardu a ofishinsa kuma ya ce bai da masaniya kan abubuwan da ke cikin takardun.

Ma’aikatar Shari’a ta nada wani mai gabatar da kara na musamman don bincika takardun da ake magana akai

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments