Hukumar hadin gwiwar ayyukan sufurin sama ta kasar China AVIC, ta ce an fara gwajin tashi da saukar jirgin sama mai sauka a ruwa wanda kasar ta kera.
Hukumar ta AVIC ta ce an kai jirage 2 samfurin AG600M na kashe gobara, dake karkashin nau’ikan jirage samfurin AG600, cibiyar gwaji dake gundumar Yanliang ta Xi’an, a lardin Shaanxi dake arewa maso yammacin kasar Sin.
AVIC ta kara da cewa, samfurin jirgin ya shiga matakin gwaji a hukumance, domin samun lasisin aiki yadda ya kamata. Ana kuma sa ran da farko, jirgin zai samu dukkanin sauye-sauye da suka dace na gudanar da gwajin inganci.
An yi wa jirgin kirar AG600 lakabi da “Kunlong”, ana kuma kera dangoginsa ne domin gudanar da ayyukan ceto na gaggawa.
Kaza lika ana iya amfani da su wajen kashe gobarar daji, da binciken teku da ceton rayuka, da ma sauran ayyukan gaggawa masu matukar muhimmanci