Babban bankin Najeriya CBN ya umarci dukkan bankunan kasuwanci na ƙasar da su fara biyan masu ajiya a bankunan sababbin takardun naira daga cikin bankunan ba kamar yadda ya umarce su da su riƙa biyansu ta na’urar cirar kuɗi ta ATM ba.
Wannan umarnin na zuwa ne bayan da harkokin kasuwanci suka kusan tsayawa cak bayan da gwamnatin Najeriya ta fitar da sababbin takrdun kuɗin na naira 200 da 500 da 1,000.
Cikin wata sanarwa da daraktan sadarwa na bankin Osita Nwanisobi ya sanya wa hannu, CBN ya ce ya lura da wasu miyagun halaye da ‘yan ƙasar ke nunawa na sayarwa, da yin jifa da sababbin takardun kuɗin a iska da tattaka su yayin wasu bukukuwa.
Nwanisobi ya ce babban bankin ya haɗa gwiwa da rundunar ‘yan sandan Najeriya da hukumar tara haraji ta ƙasar da ta EFCC domin hukunta waɗanda aka kama suna taka dokokin ƙasar, musamman waɗanda suka jibanci yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa.
Bankin ya kuma gargaɗi ‘yan Najeriya da su guji halayyar wulakanta takardun kuɗin ƙasar musamman a yayin da suke bikin zagayowar ranar haihuwa da na aure da na binne mamata.
Ya ce a ko ina takawa ko kuma wulaƙanta kuɗaɗe ya ci karo da dokar.
Domin kiyaye duk wani shakku, a bayyane yake a cikin sashe na 21 ƙaramin sashe na 3 na dokar CBN wadda aka sauya a 2007 cewa, cukurkuɗa kuɗi ko watsa su ko rawa akansu a lokacin bukukuwa zai iya janyo hukuncin biyan tara ko zaman gidan yari ko kuma duka biyun.
Ka zalika sashe na 21 ƙaramin sashe na 4 ya bayyana cewa “zai iya zama laifin da za a hukunta mutum, duk wanda aka kama yana talla ko sayar da takardun naira ko tsaba ko kuma duk wani nau’i na takardun da CBN yake ɗauka a matsayin kuɗi”.