Hukumar kare hakkin dan adam ta CNDH ta gabatar wa Majalissar dokokin kasar Niger rahotonta na shekarar 2021 wanda ke fayyace abubuwan da suka wakana masu nasaba da tauye hakkin bil adama a kasar a tsawon shekarar da ta shige.
Hukumar tace matsalolin tsaron da ake fama da su a jihohin Diffa da Maradi da Tilabery da Tahoua sun janyo tauye wa jama’a hakkoki fiye da kima inda aka gano cewa, an yi satar mutane a kalla sau 311 lamarin da ya shafi farar hula 754 ya kuma rutsa da jami’an tsaro 136. Wannan matsala ta hana dalibai 65,552 zuwa makaranta yayinda aka rufe asibitoci kusan 80 a yankunan dake fama da tashe tsahen hankula .
Haka kuma a shekarar ta 2021 hukumomi a wasu manyan da’irori sun hana jama’ar morar ‘yancin gudanar da gangami ko zanga -zanga sannan an yi ta kama ‘yan jarida da jami’an fararen hula sannan rikicin zabe ya haifar da garkame ‘yan siyasa da dama har ma da gurfanar da wasu daga cikinsu a kotu a bisa zarginsu da aikata ayyukan ta’addanci.