Hukuncin WTO, China tayi nasara akan kasar Amurka

Kwamitin kwararru na WTO wanda ya ke daidaita takkadamar dake tsakanin yankin Hong kong na kasar China  da Amurka kan batun  samar da kayayyaki na asali, ya yanke hukunci cewa, matakan da kasar Amurka ta dauka kan yadda take samar da kayayyaki sun saba wa ka’idojin WTO.

Game da wannan hukunci, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar China,  Mao Ning,  ta bayyana cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta mutunta hukuncin kwamitin kwararrun tare da daukar kwararan matakai don gyara kuskuren da ta yi.

Mao Ning ta bayyana cewa, kasar Amurka tana fakewa da batun tsaron kasa kan kasa da kasa ko yankuna, da siyasantar da batutuwan cinikayya, hakan ya sabawa ka’idojin hukumar WTO, kana ba su dace da moriyarta ba. Don haka, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta mutunta hukuncin kwamitin, da daukar matakai don gyara kuskurenta, da kiyaye tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban na WTO, da kiyaye tsarin cinikayya na duniya yadda ya kamata.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments