An shawarci alumma da su kasance masu kulawa da ‘ya’yansu musamman masu dauke da cututtuka da suka fi tashi a lokacin hutunturu,kamar,sikila da asima da sauran cututtuka.
Daya daga cikin jigo a kungiyar yankasuwar karamar hukumar kabo, Alh mamuda zangon kabo ne ya ba da shawarar a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa dake nan jihar kabo.
Zangon kabo yace, lokacin sanyi lokaci ne da alumma sai sun kasance masu kulawa da lura da iyalansu musamman kananan yara wadanda Galibi suke shiga cikin sanyi,kamata yayi su Samar musu kayayyakin da za karesu daga kamuwa da nau’in cututtuka, domin idon wata cuta ta kamasu kudin da za su kashe wajen magani yafi yawan kudaden da za su kashe wajen siyan kayan sanyi.
Yace akwai bukatar alumma su rika amfani da takunkumin rufe fuska da hula da safa da sauran abubuwan da za su kare kawunansu wajen kamuwa da sanyi,domin Allah subahanahu wata,ala ya hani bawa ya shiga cikin abubuwan da za su cutar da shi.
Mamuda zangon kabo yace,alumma da dama suna amfani da wata ko kuma nau’in kayayyakin wuta,dole sai sun zama masu kulawa da lura wajen yin amfani da wadannan kayayyakin, saboda kaucewa tashin gobara Wanda ba fatan hakan ake ba,inda yace,sau da yawa a irin wannan lokaci ana samun sakaci daga wasu mutanen musamman iyayemu mata da kodayaushe suke kulawa da gida har ma da yara.
Haka zalika,ya bukaci Gwamnatoci a matakai daban daban da su bijiro da hayoyin taimakawa masu larurar cututtuka da suka fi tashi a lokacin sanyi,kamar,Asima da cutar Amosanin jini (wato)sikila wadanda suke da wahalar sha,ani da nawainiya da yara.
Ya kara da cewa,baiwa irin wadanda nan mutane kulawa da taimako yana kara musu karfin gwiwa da karsashi a rayuwarsu ta yau da kullum,inda rashin basu Agaji da taimakon gaggawa yana sanyasu cikin damuwa da tashin hankali wajen gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum,Wanda kuma hakan bai kamata ba.
Daga karshe yace,Gwamnati da masu ruwa da tsaki da masu hannu da shuni suna da rawar takawa domin tallafawa masu dauke irin wadanda cututtuka dake da wuyar sha,ani wajen yin magani daga talakawa har masu arziki.
Ibrahim sank gama pyramid radio.