Hukumar hisbah ta jihar Kano ta dira a tashoshin motar da yammatan da suke tallah suke yada zango don tafiya gidajen su.
Mataimakiyar kwamandan hukumar a bangaren mata malama khulsum kasim ita ce ta jagoranci Jami,an hisbah mata domin yiwa yammata masu tallace tallacen nasiha akan su kaucewa kaiwa dare a wuraren tallan.
My administration will not disappoint peoples of Kano state : Gawuna
Malama khulsum kasim ta nuna rashin Jin dadinta da sakacin da iyaye sukeyi da ya’ya mata ta hanyar yin talla tun daga safiya har zuwa dare ba tare da sun damu ba.
Sarkin tashar sabon titin fanshekara malam sunusi kwankwaso yace zasu bawa hisbah hadin Kai domin dakile tallan dare.
kwamandar sashen mata ta yi musu nasiha tare da jajjada musu cewa in suka kai karfe shida na magaruba to ba shakka hukumar zata fara kamasu