Shugabannin rundunonin sojin kasashen kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afrika (ECOWAS), sun kaddamar da taro a ranar Litinin, a Bissau babban birnin kasar Guinea-Bissau, domin tattauna dabarun yaki da ta’addanci da juyin mulki.
Wata sanarwa da shugaban rundunar sojin Guinea Bissau, Janar Biague Na Ntan ya fitar, ta ce daya daga cikin sakamakon da ake sa ran samu daga taron shi ne, gabatar da tsarin ayyukan rundunar sojin ko-ta-kwana ta ECOWAS, wajen yaki da ta’addanci.
A cewar Janar Na Ntan, za a iya amfani da rundunar ko-ta-kwana ta ECOWAS wajen yaki da ta’addanci da dawo da kundin tsarin mulki a yankin, idan aka fuskanci barazana.