Rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar Taraba ta tabbatar da mutuwar jamian ta guda biyu tare da jikkata wasu biyo bayan barkewar wata hatsaniya a garin Jalingo
Jami’in hulda da jama’a na rundunar Abdullahi Usman, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a birnin Jalingo
Usman Ya ce tuni kwamishinan yan sanda na jihar Yusuf Suleiman da kwamandan bataliya ta shida Brigade, Brig. Gen. Frank Etim sun gana domin shawo kan lamarin