Abubuwa takwas da ya dace ku sani game da zababben gwamnan kano

Ranar litinin ne hukumar zaɓe mai zaman kanta ta sanar da Abba Kabir Yusuf wanda ake yi wa laƙabi da Abba gida-gida a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano.

Ga abu takwas da ya kamata ku sani a kansa:

An haife shi ranar 5 ga watan January, 1963 a ƙaramar hukumar Gaya ta jihar Kano.

Ya yi karatun Firamare a makarantar gwamnati da ke Sumaila Primary School sannan kuma ya yi karatun Sakandire a makarantar gwamnati ta Lautai a Gumel da ke jihar Jigawa.

Abba ya yi karatun difloma a kwalejin kimiya da fasaha ta Mubi sai kuma babbar difloma a kwalejin kimiya da fasaha ta Kaduna watau Kaduna Polytechnic.

Ya yi karatun digirinsa na biyu digiri a jam’iyyar Bayero ta Kano a fannin harkokin kasuwanci.

Tsohon kwamishinan ayyuka a jihar Kano a zamanin mulkin Rabi’u Musa Kwankwaso.

Abba gida-gida ya yi takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar Kano a shekarar 2019 amma bai samu nasara ba.

Yana da mata biyu da ‘ya’ya da dama.

Ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kano a ranar 20 ga watan Maris na 2023

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments