Kazamin rikicin da ake tafkawa tsakanin rundunar sojin Sudan da rundunar RSF, ya yi sanadin rayuka akalla 528 da raunata wasu 4,599.
Rahoton da ma’aikatar lafiya ta kasar ta fitar jiya, ya ce tsawaita tsagaita bude wuta ya sa yanayi ya lafa a yawancin jihohin kasar, in ban da yammacin Dafur da babban birnin kasar wato Khartoum.
A cewar rahoton, an kara yawan cibiyoyin bada kiwon lafiya a Khartoum, kana an inganta yanayin tuntubar asibitoci.
Ma’aikatar ta kara da cewa, ana aiwatar da shirye-shirye ta yadda wasu kasashe abokan huldar Sudan da hukumomin kasa da kasa da na shiyyoyi, za su samar da kayayyakin jinya ga mutane mabukata.
Yayin da rikici tsakanin rundunonin biyu ya shiga mako na 3, kasashen duniya na gaggauta kwashe mutanensu daga kasar, yayin da dubban al’ummar Sudan ke tserewa rikicin.