Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, a ranar Asabar, 12 ga watan Nuwamba, ta yi martani kan rahoton cewa tana bincike kan zargin safarar miyagun kwayoyi kan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, rahoton Vanguard.
A cikin wani sanarwa da hukumar ta fitar da Legit.ng ta gani, ta yi kira ga yan Najeriya su yi taka tsantsan da ikirarin cewa INEC na hadin gwiwa tare da gwamnatin Amurka don binciken zargin da ake yi wa Tinubu.
Hukumar ta ce wannan sanarwar da ya bazu ba daga INEC ya fito ba kuma hukumar zaben ba ta bincikar Tinubu kan zargin safarar miyagun kwayoyi, PM News ta rahoto.
Sashi na sanarwar ya ce: “Wata sanarwar manema labarai da aka ce hukumar ta fitar na ci gaba da bazuwa a intanet tun jiya Juma’a 11 ga watan Nuwamba 2022.
“Yana ikirarin cewa hukumar ta fara bincike kan batun kwace kadarori don laifi daga daya cikin yan takarar shugaban kasa a babban zaben da ke tafe kuma tana hadin gwiwa da kotu a Amurka kan batun don duba yiwuwar saba dokokin zabe na 2022.