Wa ya kamata na tsayar mataimaki na a zabe mai zuwa : Bola Tinubu
Daga Kabir A. Dukawa
Dan takarar shugaban Kasar Nageriya Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, ya bayyana cewa har yanzu bai fidda wanda zai masa mataimaki ba a takarar da yake yi na shugaban Kasa a zaben 2023, mai zuwa.
Tinubu ya bayyana haka ne a yayin kaddamar da wani littafi da aka wallafa na bikin cikar shekaru 60, da haihuwar shugaban majalisar wakilai Mista Femi Gbajamiamila, da aka gudanar ranar Lahadi a Abuja.
Daga cikin jawaban da ya gabatar Tinubu yace har yanzu yana laluben mutumin da ya dace ya zama mataimakin sa domin gudanar da mulki na gari a Kasar nan.
Tinubu wanda yanzu haka yake da mataimaki na wucin–gadi Masari, kuma yana da damar zabo wanda zai masa mataimakin kafin ranar 15, ga watan Yuli, kamar yadda hukumar zabe ta Kasa ta tanada.
Tinubu daga karshe ya gode wa Kakakin majalisar ta wakilai Mista Gbajamiamila, bisa irin gudun mawar da ya bashi a lokacin gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar APC ta Kasa.