Kungiyar kasuwar hada hadar wayoyin hannu dake farm centre Tasha alwashin hada hannu da Bankuna domin samarwa yayan kungiyar rancen jari dan bunkasar tattalin arzikin kasuwar.
Shugaban Kungiyar dake farm Center Alhaji Hassan Abubakar Abdullahi ne ya sanar da hakan azantawarsa da manema labarai a ofishinsa dake nan kano.
Alhaji Hassan Ya bayyana cewar sun gayyato Bankuna kuma sun zauna da su domin baiwa yayan kungiyar rancen, jari wanda daga cikinsu akwai Bankin Wema bank,Unity bank ,Sterling bank da dai sauran bamkuna da dama don bunkasar tattalin arzikin kasuwar.
Shugaban ya yabawa yayan kungiyar bisa nuna kishin su kan yadda zasu dogara da kansu da kuma hadin kai da goyon baya dari bisa dari da suke baiwa kungiyar.
Dangane da shaanin tsaro kuwa Alhaji Hassan Ya yabawa Kwamatin tsaro da hukumomin tsaro a kasuwar bisa yadda suke aiki tukuru Wajen tsaftace kasuwar daga batagari masu saye da sayar da wayoyi da naura mai kwakwalwa na sata.
Kazalika Ya bayyana cewar kasuwar su ta lashe gasar tsafta kasancewar duk lokacin da ka shigo kasuwar ba zaka ga tarin Shara a kasuwar ba saboda Kwamatin kasuwar yana aikinsa yadda yakamata.
Daga karshe yayi kira ga gwamnati kan ta taimaka ta cike ramukan dake kan titinan kasuwar domin saukakawa ababen hawa dake shige da fice a kasuwar.