Al’ummar kasan nan su yi matukar kadowa sakamakon rashe babban dankasuwa, dan siyasa kuma Malamin Addinin Musuluchi Alhaji Uba Leader. A ranar Asabar 21 ga watan August, 2022 Allah Ya yi wa marigayin rasuwa bayan ya yi fama da gajeriyar rashe lafiya a Asibitin Zenith Clinic da barin Kano.
Kafin rasuwarsa shi ne shugaban Kamfane Masaka Texts stall dake unguwar Gwammaja a jihar Kano
Shi ma Shugaban Kasar Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyarsa ga ‘iyale da ‘yan uwa da saurar al’ummar kasannan musamman ma Na jihar Kano, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu ya rabawa manema labarai, a Abuja yace shugaban ya yi matukar kaduwa bisa wannan babban rashi.
Alhaji Uba Leader, ya rasu ya bar ‘yan 34 maza da mata da kuma jikoki da dama, tuni a ka yi jana’izarsa kamar yadda Addinin Musuluchi ya tanada