Gwamnatin tarayya da ta jihohin kasar nan suna da laifi wajan rashin dai-dai ta farashin Dala dana kayan masarufi.

Alumma da dama na ci gaba da kokawa a bangaran hada_hadar kudaden kasashen ketare, musamman Dala wadda da itane yankasuwar dake fita zuwa kasashen Duniya suke amfani domin yin kasuwanci, hakan ya janyo babu tsayayyen farashi da za ka dauka a matsayin farashinta.

Shugaban kungiyar matasan yankasuwa na fannin magungunan Asibiti dake Malam Kato anan jihar Kano, Alh.Mamuda Zangon Kabo yayi kira ga Gwamnatin tarayya da sauran masu Ruwa da tsaki a fannin hada_hadar kudaden kasashen ketare, da su kawo wasu hanyoyi da za su taimakawa yankasuwa dake zuwa kasashen ketare domin harkokin kasuwanci duba da tashin gwauran zabin da Dalar take yi a fadin kasar nan.

Yace,Gwamnatin tarayya tana da rawar takawa a fannin kawo sauyi na kudaden kasashen ketare, inda yace yankasuwa suna mutukar shan wahala saboda rashin samun kudaden kasashen ketare da suka hadar da Dala da Euro da yans na kasar sin, da sauran kudaden kasashen waje da alummar Najeriya suke amfani da su domin yin kasuwanci da yawan Neman lafiya da na shakatawa.

Mamuda Zangon Kabo, ya kara da cewa:ya kamata Gwamnatin tarayya da ta jihohin Najeriya su yi duk maiyiyuwa wajen bullo da hanyoyi da za su kawar da irin wadannan matsaloli na rashin daidaituwar kudaden kasashen Duniya.

Daga karshe ya bukaci Gwamnati da ta rika karbar shawarwari daga daidaikun alummar Najeriya, kasancewar akwai dubban masu ilimin da za su taimakawa mahukunta da hanyoyin da za su Samar da hanyoyin mafita a harkokin kudaden kasashen ketare da kawo bunkasar tattalin arziki a Najeriya da kuma,jihohin su.

(Cov/Ibrahim Sani gama )

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments