Masana a jami’ar Cambridge ta kasar Birtaniya sun kaddamar da sakamakon nazarinsu a kwanan baya, inda suka ce, shan ruwa, shayi ko kofi marasa sukari a maimakon ruwan lemu da aka sarrafa ko ruwan madara mai sukari, zai taimaka wajen rage barazanar kamuwa da ciwon sukari mai nau’in 2.
Ruwan lemu, wani irin abin sha ne da aka sarrafa ba tare da barasa ba, inda a kan sa sukari a ciki.
Masu nazarin sun nuna cewa, shekaru da dama da suka wuce, suka fara gudanar da wani bincike na samfuri tsakanin masu aikin sa kai fiye da dubu 25, wadanda shekarunsu suka wuce 40 amma ba su kai 80 a duniya ba. A cikin shekaru 11 da masu nazarin suka dauka suna gudanar da nazarin, sun bukaci masu aikin sa kan da su rubuta al’adarsu ta ci da sha a ko wace rana, musamman ma yawan sukarin da suka sha. Yayin da suka kawo karshen nazarin, wasu 847 daga cikin wadannan masu aikin sa kai sun tabbatar da kamuwa da ciwon sukari mai nau’in 2.
Masu nazarin sun tantance bayanai, tare da yin kidaya, a karshe dai sun gano cewa, idan masu aikin sa kan sun sha ruwa, shayi ko kofi marasa sukari, a maimakon ruwan lemu a ko wace rana, barazanar da suke fuskanta wajen kamuwa da ciwon sukari mai nau’in 2 ta kan ragu da kaso 14. Kana kuma, idan sun sha ruwa, shayi ko kofi mara sukari, a maimakon ruwan madara mai surkari a ko wace rana, barazanar ta kan ragu da kaso 20 zuwa 25.
Masu nazarin sun yi nuni da cewa, sakamakon nazarinsu ya kusan yin daidai da sakamakon nazarce-nazarcen da aka gudanar a baya, sa’an nan ya samar da shaida na daban kan shawarar da hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa wato WHO ta gabatar, dangane da kayyade yawan sukari da ke cikin abinci da abin sha