Hukumar hisbah ta jihar tayi kira ga al’umma dasu yi taka tsantsan akan labarurrukan da suke futa daga bakunansu.
Babban kwamandan hisbah sheik Haroon Muhammad sani ibn sina shine ya bayyana hakan ga manema labarai a shalkwatar hukumar hisbah a cigaba da bayaninsa na goron juma,a.
Sheik ibn sina yace abin ya zama tamkar wata masifa yadda wasu ke tutiya da tura labari ko al’fahari da ganin sun zama a sahun gaba wajen yada labarin jita jita wanda yace akwai narko na azaba da Allah zai yiwa masu irin wannan hali.
Wakiyarmu Jamila sulaiman Aliyu ta bamu labarin cewa kwamandan hisbah ya roki al’umma dasu tseratar da kansu daga yada labari komai sahihancin sa matukar bazai zamewa al’umma alkhairi ba.
ya kuma ce masu rige rigen tura labari a kafaren sada zumunta da kuma zaman majalisa da teburin mai shayi da kuma mata masu yada jita jita a wuraren buki ko suna da sauran tarurruka su sani sawa bakuna su linzami ko takunkumi yafi alkhairi .