taron na yini biyu an gudanar domin hada kan al’umma da dakile tarzoma a tsakankanin magoya bayan jam’iyyun siyasa daban daban bisa tunkatowar zabaubbukan dake tafe.
Mr Charles shine jagoran taron yace sunzo kano domin su tattauna da masu kula da ganin zaman lafiya ya samu a tsakanin al’umma a matakin jiha (CMMRC) da kuma na mazabu dake kananan hukumomi dan ganin an dakile duk wata hatsaniya da kuma samun nasarar zabe da nusar da al’umma irin matakan daya kamata su bi don samun nasarar wannan taron.
Shugabar cibiyar Samar da zaman lafiya a jihar Kano Hajiya Ramatu Adamu ta mika rokon ta ga mahalatta taron dasuyi abinda ya dace a matakin mazabu da kananan hukumomi da jiha baki daya .
Hajiya Ramatu Adamu ta kuma ja hankalin masu shiga tsakanin a harkar zaman lafiya (CMMRC ) da masu taimaka musu a matakin mazabu (CPO,s) dasu hada kai a kungiyance tare da samun shaida a gwamnatance domin samun biyan bukata.
A jawabin sa shugaban sashen cigaban al’umma na karamar hukumar nassarawa Alhaji Hassan Garon ya bayyana cewa yawaitar kungiyoyi zai taimakawa gwamnati a zaben dake gabatowa zasuyi tasiri idan har suna da rigista daga hukuma sannan ayyukansu zasu samu karbuwa.
Alhaji hassan Garo ya bayyana cewa su nemi ilmin al’amarin daya shafi samawa kungiyoyi shaida daga wurin masana.