Wata mota da ta dauko man fetur tayi hadari a gadar Ankpa inda aka samu wani mummunan hadari ya yi sanadiyyar dinbin mutane sun mutu
Lamarin ya faru ne a wata gada da ke garin Ankpa, jami’an FRSC sun tabbatar da afkuwar lamarin
Fiye da mutum 20 ake tunani sun rasa rayukan su sanadiyar kifewa da wata babbar mota tayi a kan wata gada a jihar Kogi.
Jaridar Daily Trust tace a safiyar Alhamis, 29 ga watan Satumba 2022. babbar mota ta fadi a wata gada da ke kan ruwan Maboro a karamar hukumar Ankpa a jihar Kogi.
Motar ta dauka man fetur ne yayin da taki sarrafuwa a hanun direbanta, tayi hadari a kan titi.
Wani wanda abin ya faru a gaban idanunsa, ya shaidawa manema labarai cewa motar tayi hadari da kimanin karfe 3:30 na yamma.
“Babu wanda ya san adadin mutanen da suka mutu yanzu haka. Mutane suna cikin rafin suna harkokin gabansu, sai motar ta kubuce. Daga nan ta fai, ta tarwatse a kan gadar. Abin babu kyawun gani. Mafi munin abin da na taba gani tun da nake a rayuwata.” – Inji Usman Ahmed dake zaune a garin Ankpa .