Attajirin da ya yanka mutane 800,000 a Rwanda zai gurfana a gaban kotun Duniya.

Attajirin da ake zargi da yanka dubban mutane a Rwanda zai gurfana a kotu.
Daga Walid Hari

Daya daga cikin manyan mutane na karshe da ake zargi a kisan kiyashin da aka yi a Rwanda a 1994 zai gurfana a gaban kotun duniya da ke birnin Hague a yau  Alhamis.

Felicien Kabuga na fuskantar tuhumar aikata kisan kiyashi da laifukan cin zarafin bil-Adama, a kan irin rawar da ake zargin ya taka wajen yanka ‘yan kabilar Tutsi da ‘yan Hutu masu sassaucin ra’ayi har dubu dari takwas (800,000).

A farkon gurfanarsa gaban kotun a 2020, lauyoyin Mista Kabuga, sun musanta laifukan da ake tuhumarsa da su.

Ana sa ran ya gurfana da kansa a gaban kotun ta duniya a zaman ta na Alhamis.

Tsawon gomman shekaru Felicien Kabuga ya kasance daya daga cikin mutanen da ake nema a duniya ruwa a jallo.

Masu gabatar da kara sun ce Mista Kabuga na gudanar da wata tashar rediyo, wadda ta rika yada kalaman kyama da haddasa gaba, wadanda ake bayyana ‘yan kabilar Tutsi a matsayin kyankyasai tare da angiza ‘yan Hutu kan su hallaka su duk inda suke.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments