Wani matashi ya faki numfashin Budurwarsa ya sace mata Dubu 80

Daga Dantala Uba Nuhu Kura

Wani Matashi Mai-Suna  Mustafa Abdullahi Mai-Sanaar Adaidaita Sahu Ya Fada Ragar Jamian Tsaro Yayin Da Masoyiyarsa Abar Begensa Kuma Wacce Suke sheke Aya tare Maisuna Humaira Muhamd :Yar Asalin Garin Bauci tayi karar sa.

  Humaira Wacce Ke Da Matsuguni a Kasuwar Kwanar Gafan a Karamar hukumar Garun-Mala ta Kai saurayin dadiron nata Kara ne bisa zargin sa da Yaudararta da kuma Shirya Mata Gadar Zare.

A  Cewar  saurayin nata ya bata shawara ta Haka Rami a Cikin Dakinta Na Bukka Dake Cikin Kasuwar domin ta rika Tara yan Kudaden da take samu a rami Tana Bunnewa  Batare Da Kowa Ya Saniba a Matsayin Sabon Asusu.

Nan Take Humaira ta Amincr Da Shawarar Tasa Saidai Bayan Ta  Haka Ramin Ta Fara Zuba Kudi kuma kudade sun fara kankama sun Kai kimanin dubu Dari Gogan Naka ya sadada Ya Tone Ramin Ya Kuma Kwashe kudin Baki Daya.

  Sai dai bayan gabatar da shi a gaban jamian tsaro tuni ya amsa laifin sa inda basuyi wata-wata ba suka ingiza Keyarsa Gaban Kotun Shariar Musuluncin Ta Kura wadda Mai-Sharia Malam Ibrahim Isa Usman yake jagoranta.

    Bayan Maigabatar Da Kara Insifecta Maaji Ya Karanta Masa Takardar Tuhuma
Nan Take Ya Amsa Laifinsa
Maisharia Da Ya Tambayeshi Cewar Kaiko Me Kayi Da Kudin Cewa Yayi Gyaran Babur Yayi Sauran Ya Kuma Kashe.

       Sakamakon Kurewar Lokaci Insifecta Maaji Ya Bukaci Kotu Da Ta Daga Sahariar Zuwa 22/10/2022 dan Cigaba Da Zaman Shariar

   Maisharia Tuni ya Damka wannan matashi Ga Jamiin Gidan Ajiya Da Gyaran Hali Insifecta Awwalu Muhammad Danhasan.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments