Kungiyar gwamnonin ci gaba ta tabbatar da goyon bayanta ga matakin shugaban kasa, Bola Tinubu, kan tallafin man fetur
Shugaban gwamnonin APC kuma gwamnan Imo, Hope Uzodinma, shi ne ya bayyana haka bayan ganawa da shugaba Tinubu a Aso Rock
Ya kuma nuna damuwarsa kan yadda farashi ya yi tashin gwauron zabo lokaci guda daga jin kalaman Tinubu a wurin rantsuwa
Sai dai gwamnonin sun bayyana takaicinsu bisa tashin farashin litar mai farat ɗaya biyo bayan kalaman shugaban kasa a wurin bikin rantsuwar kama aiki.
Da yake hira da ‘yan jarida jim kaɗan bayan ganawa da shugaban ƙasa, shugaban ƙungiyar gwamnonin ci gaba kuma gwamnan Imo, Hope Uzodinma, ya yi Alla-wadai da ƙara farashin.