Tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya kare hukuncin da Shugaban kasa Bola Tinubu ya dauka na cire tallafin man fetur, cewa ba abu mai sauki bane shugabantar kasa irin Najeriya.
Wike ya bayyana hakan ne a wata takaitacciyar hira da yayi da manema labarai na fadar shugaban kasa a ranar Juma’a da ta gabata.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Wike da Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo da tsohon Gwamna James Ibori na jihar Delta sun gana da shugaban kasar a fadar shugaban kasa a ranar Juma’a.
Da yake martani ga wata tambaya kan dalilin ziyarar nasu, Wike ya ce:
“Babu wani babban abu game da shi, gwamnan na jihar Oyo ya fada maku abun da muka zo yi; basa goyon baya.
Muna goyon bayan duk shawarwari da ya yanke, ya nuna cewa ya shirya ma aikin kuma babu abu game da hakan. yana bukatar daukar tsauraran matakai don kasa ta ci gaba.”500