Gwamnoni biyar na jam’iyar PDP sun gana da juna a birnin Lagas

Gwamnonin PDP biyar sun zauna da wasu manyan jiga-jigai da fusatattun ‘ya’yan jam’iyyar a jihar Legas

Ana tsammanin bayan sun tattauna ci gaban da ke jam’iyyar a yanzu, gwamnonin na G5 zasu san matakin dauka na gaba

Babbar jam’iyyar adawar kasar dai na fama da rikici wanda yaki ci yaki cinyewa gabannin babban zaben 2023

Wata majiya da ke da masaniya kan taron, ta ce taron zai ba Wike da hadimansa damar sake bitar ci gaban da aka samu na baya-bayan nan a jam’iyyar kafin su dauki mataki na gaba.

Kamar yadda jaridar New Telegraph ta rahoto, ana sa ran Gwamna Wike da mukararrabansa za su yi jawabi ga manema labarai bayan taron.

Gwamnonin G5 da ake sa ran zasu halarci taron sun hada Nyesom Wike na jihar Ribas, Samuel Ortom na jihar Benue, Seyi Makinde na jihar Oyo, Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu da kuma Okezie Ikpeazu na jihar Abia.

Sauran mahalarta taron sune tsohon gwamnan jihar Ondo, Dr Olusegun Mimiko, tsohon gwamnan jihar Ekiti, Mista Ayo Fayose, tsohon gwamnan jihar Cross River, Mista Donald Duke.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments