Majalisar Dinkin Duniya ta fara tattauna kan bukatar baya-bayan nan ta ganin an baiwa kasashen Afrika damar samun kujerar dindindin a kwamitin tsaro na Majalisar.
Kiraye-kirayen kasashen Afrika na zuwa ne a dai dai lokacin da Majalisar ta bayyana shirin bukatar fadadawa tare da kara yawan mambobin kwamitin tsaron musamman wadanda ke da kujerar dindindin.
Yanzu haka dai ana ci gaba da tafka muhawara kan yiwuwar baiwa nahiyar ta Afrika kujerar dindindin a wani yunkuri na basu karfin ikon tsoma baki ko kuma bayar da gudunmawa wajen cimma matsaya kan lamurran da suka shafi tsaro da zaman lafiyar Duniya.
Jakadan China a Majalisar da ke da kujerar dindindin a kwamitin tsaron, Zhhang Jun ya ce garambawul din da Majalisar ke shirin yiwa kwamitin zai kara yawan wakilcin kasashen Afrika baya ga basu kujerar dindindin wadda za ta kawo karshen rashin adalcin da aka shafe shekaru ana musu.
Alie Kabba jakadan Sierra Leone a zauren ya ce na bukatar muryar da za ta rika bayyana ra’ayoyinta game da hukunce-hukuncen da ake zartaswa a kwamitin da galibi ke shafarta.