Kungiyar masu kera motoci ta kasar Sin ta ba da sabuwar kididdiga cewa, a farkon watanni 10 na bana, yawan motoci masu amfani da wutar lantarki da Sin ta samar da kuma sayar da su sun kai kimanin miliyan , kuma sha’anin na ci gaba da samun karuwa.
A cikin wadannan watanni 10, yawan motocin da aka samar aka kuma sayar, ya kai miliyan 5.4 da miliyan 5.3 bi da bi, wanda ya ninka sau 1.1, kuma ya kai matsayin koli a tarihi.
Yayin da ake kokarin habaka kasuwar cikin gida dangane da wannan fanni, yawan motocin da aka fitar zuwa waje kuwa ya ci gaba da karuwa. Alkaluman da aka fitar na nuna cewa, a shekarar 2021, yawan motocin da Sin ta fitar ya kai dubu 310, wanda ya ninka sau 3 bisa na makamanci na shekarar 2020. A farkon watanni 10 na bana, yawan motocin da aka fitar zuwa ketare, ya kai dubu 494, wanda ya karu da kashi 96.7%