Kamfanin Man fetur na kasa wato NNPCL, ya bada Sanarwar kama wani jirgin dakon Mai da ke hanyarsa ta zuwa Kamaru dauke da danyan Man fetur da aka haka daga jihar Ondo lita dubu 800.
Cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Litinin, ya ce jirgin mallakin wani kamfanin kasar nanmai suna MT-TURA II, ya kai shekaru 12 ya na dakon irin wannan Man a boye, kuma a yanzu za a lalata jirgin don ya zamar wa masu irin wannan sana’a darasi.
Sanin kowa ne cewa Bangaren man fetur na kasar nanna fama da rashawa tsawon shekaru, inda ake satar danyen mai da kuma kafa haramtattun matatun mai a yankin Neja-Delta.
A shekarar 2022 gwamnatin kasar nan karkashin jagorancin Muhammadu Buhari ta ce tana asarar sama da gangar danyen mai 470,000 a kowace rana sanadiyyar wadannan ayyuka na barayin danyen Mai.
A watan Agusta shekarar 2022 danyen man fetur da Najeriya ke fitarwa sai ya ragu zuwa kasa da ganga miliyan guda a kowace rana – mafi karanci a tarihin hakar danyen Mai cikin shekaru 30.