Masu aikin ceto suna bincike a gaɓar ruwan tsibirin Canary saboda wani jirgin ruwan da ke ɗauke da ‘yan ci-rani aƙalla 200 daga Afirka da suka ɓata fiye da mako ɗaya.
Ƙungiyar ba da agaji mai suna Walking Borders ta ce jirgin masunta da ke tafiya daga Garin Kafountine, dake gaɓar teku a kudancin Senegal da ya kai kilomita 1,700 daga Tenerife.
Ƙungiyar ta ce akwai ƙananan yara da yawa a ciki, kamar yadda rahotanni daga kamfanin dillancin labaran ƙasar Sifaniya suka ambato.
Akwai irin wannan jirgin ruwa guda biyu ɗauke da gomman mutane da su suka ɓace.
Ma’aikatan ceto a teku na ƙasar Sifaniya sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na EFe cewa wani jirgin sama ya shiga sahun aikin bincike.
Jirgin ruwan mai ɗauke da mutum 200 ya bar Kafountine ranar 27 ga watan Yuni inda ya nufi tsibirin Canary.