Biyo Bayan zargin yin karan tsaye ga dokar kasa da ta aikin gwamnati a hukumar DSS da ake ganin gwamnan jihar Kano Dacta Abdullahi Umar Ganduje, yayi wajen rike shugaban hukumar Muhammad Alhassan na hana shi yin ritaya tsawon watanni 15 da suka wuce yanzu haka jam’iyar NNPP ta shirya gudanar da Zanga-zangar lumana
A cewar guda daga cikin manyan jam’iyar kuma wanda yayi mata takarar kujerar sanatan Kano ta tsakiya Baffa Bichi, gwamna Abdullahi Umar Ganduje yana so yayi amfani da hukumar DSS ne wajen haifar da tashintashina a zaben jihar Kano domin ya Sami damar gudanar da magudi.
Bichi yace da Alhassan Ganduje yayi amfani a zaben 2019 inda ya sauya wa kanawa zabin su.
Kazalika yace kasancewar suna da alaka ta abota da gwamnan jihar kano Dacta Abdullahi Umar Ganduje, tun a shekarar 2017 yayi kulle-kullen sa aka dauke shugaban hukumar DSS na wannan lokacin kuma aka maye gurbin sa da wannan abokin nasa
Ya kara da cewa tuni sun aike da sako zuwa ga shugaba Buhari da shugaban hukumar DSS na kasa domin su ji da lamarin